‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutane 16 a kauyen Goni Gora da ke Jihar Kaduna sun bukaci kudin fansa kafin sakin mutanen.

‘Yan bindigan sun bukaci da a basu naira Tiriliyan 40, da Babura 150 tare da motoci kirar Hilux guda 11 kafin sakin mutanen.
Wani shugaban al’ummar yankin John Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da Jaridar Nation a jiya Litinin.

Yusuf ya ce da fari maharan sun fara yin garkuwa da mutane uku a kauyen kafin daga bisani kuma suka dawo suka yi garkuwa da mutane 13 a ranar Laraba.

Shugaban ya kara da cewa duk a cikin mako guda maharan suka yi garkuwa da mutanen a wasu hare-hare da su ka kai cikin kauyen.
Shugaban ya nemi mahukunta su kawo musu dauki, tare kuma da kafa sansanin soji a dazukan da ke kewaye da kauyen wanda ya hada kauyen da Birnin Gwari.
‘Yan ta’addan na neman kudin fansar ne kwanaki hudu bayan ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu daliban makaranta 287 a kauyen Kuriga da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar.
