Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi martani kan kisan sojoji 16 da aka yi a wani kauye da ke jihar Delta.
Tinubu ya bai wa hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa umarnin zakulo wadanda ke da hannu a kisan tare da hukunta su.
Har ila yau, shugaban ya ba da umarnin makamancin wannan ga hedkwatar tsaron da ke birnin Abuja domin bincike mai tsauri.
Shugaban ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da sanya wa hannu a jiya Lahadi 17 ga watan Maris.
Ya ce kai hari kan jami’an sojoji kamar aiwatar da hari ne kan kasar baki daya inda ya ce ba zai lamunci haka ba a mulkinsa.
Ya kuma tura sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da abokan aikinsu da kuma masoyansu baki daya.


