Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Garkin Block da ke Maiduguri a Jihar Borno.

A cewar wani ganau, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5:00 na safiyar yau Talata.


Ya ce, cikin kankanin lokaci wutar ta bazu cikin sansanin, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.
Sai dai hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) ta ɗauki mataki kan lamarin, inda jami’an kashe gobara suka isa da misalin ƙarfe 5:25am domin kashe gobarar.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a iya tantance girman barnar da gobarar ta yi ba, haka kuma, ba a gano musabbabin tashin gobarar ba daga bangarorin da abin ya shafa ba.
Sansanin ’yan gudun hijira na Garkin Block na nan a kan hanyar Madinatu da ke cikin birnin Maiduguri a jihar Borno.