Babban Bankin Najeriya (CBN) ya biya bashin dala biliyan 7 da gwamnan bankin, Yemi Cardoso ya gada bayan shigarsa ofis a shekarar 2023.

Daraktar yada labaran bankin, Hakama Sidi Ali ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Laraba 21 ga watan Maris.


Hakama ta tabbatar da biyan dukkan basukan wanda ake ganin zai iya saka darajar naira ta tashi a kasuwar duniya.
Ta ce bankin ya dauki wani kamfanin kula da kudi mai suna Deloitte Consulting da zai tabbatar da biyan bashin ga wadanda suka cancanta kadai.
A bangare guda kuwa, gwamnan bankin CBN, Yemi Cardoso ya bayyana amfanin biyan bashin domin ɗaga darajar naira.
Wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ke dauka domin tabbatar da inganta darajar naira a kasar.
Masana na ganin wannan zai kara inganta tattalin arzikin kasar tare da dakile tashin farashin kayayyaki musamman kayan da ake shigo da su daga waje.