Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roki ƴan majalisar wakilai da su rage kiran ministoci da shugabannin hukumomi domin bayyana a gaban kwamitocin majalisar.

 

Shugaba Tinubu ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗe baki tare da kakakin majalisar, Tajudden Abbas da sauran shugabannin majalisar.

 

An dai shirya buɗe bakin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Maris, a faɗar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, Abuja.

 

Tinubu ya ce yayin da sanya ido kan ayyukansu yana da muhimmanci domin tabbatar da gaskiya, yawan kiransu ka iya kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

 

Maimakon kiran, sai ya buƙaci ƴan majalisun da su riƙa kula sosai wajen gudanarwa tare da sa ido kan ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: