Majalisar wakilai ta amince da sabuwar dokar ƙarin albashi da alawus ga babban joji na ƙasa (CJN) da sauran alƙalan kotunan Najeriya.

 

Manema labarai sun ruwaito cewa idan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar, babban joji na ƙasa zai riƙa samun albashi da alawus na milyan 64 a ko wacce shekara.

 

A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya aikawa majalisar tarayya bukatar ƙarin albashi ga alkalai da ma’aikatan shari’a.

 

A yanzu babban joji na ƙasa (CJN) zai riƙa ɗaukar albashin N1,121,884.83 a kowanne wata.

 

Akwai kuma alawus na N4,263,162.35 a kowanne wata da alawus din N6,731,308.98 wanda zai riƙa samu akai akai.

 

A yayin da ya kai matakin ritaya kuwa, zai samu giratuti na N80,775,707.70, da bashin mallakar mota na N53,850,471.80

 

Alƙalan Kotun Ƙoli za su rika daukar albashin naira N826,116.19 a kowane wata da alawus na N4,213,192.

 

Akwai alawus na hayar gida na N9,913,394.22 da kuma giratuti na N29,740,182.65 idan sun yi ritaya.

 

Akwai alawus na kayan gida da na bashin mota da ya kai N39,653,576.88.

 

A yanzu alkalan Kotun Daukaka Kara za su rika samun albashin N665,475.97 a kowanne wata, da alawus din N3,726,665.40 na wata wata.

 

Akwai alawus na hayar gida da ya kai N7,985,711.58 da kuma N23,957,134.74 a matsayin kudin giratuti idan sun yi ritaya.

 

Za a ba su N31,942,846.32 a matsayin lamunin sayen mota da kudin gyaran gida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: