Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda ya tarar da yadda rabon abincin ciyarwa ke gudana ga mabukata a watan Azumin Ramadan.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a jiya Juma’a.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai daya daga cikin guraren da ake ciyarwar a gidan maza da ke karamar hukumar birni a Jihar.

Abba ya ce wadanda suke rabon ciyarwar, ba sa bai’wa wadanda aka yi abin dominsu, duk da wadatattun kayan abincin da aka bai’wa kowanne guri.

Gwamnan ya ce bayan halartar gurin ya bayar da umarnin gudanar da bincike, tare da canja wadanda suke gudanar da rabon.