Ministan ilimi a Najeriya Farfesa Tahir Mamman y ace gwamnati bat a biya kuɗi fansa ba kafin sakin ɗaliban da ƴan bindiga su ka sace a ƙaramar hukumar Kuriga ta jihar Kaduna.

Ministan ya bayyana haka ne a yau Litinin yayin wani taro da aka gudanar a Abuja bayan da aka saki ɗaliban su 137 kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta shaida.
Ministan ya yabawa shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da jajircewar da yaui wajen ganin an kuɓutar da mutane.

Helkwatar tsaro a Najeriya ma ta tabbatar da cewar an samu ɗaliban ne a jihar Zamfara bayan da aka sacesu daga makarantarsu a jihar Kaduna.

Al’amarin satar ɗaliban ya ɗauki hankali, wanda kafin shi, said a ,yan bindiga su ka sace wasu ɗaliban stangaya a jihar Sokoto.