Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar yin luguden wuta a maboyar wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram ne a yankin tafkin Chadi,

Rundunar ƙarƙashin Operation Hadadin Daji ne su ka kai harin ta sama, tare da kasha da dama daga mayaƙan a yankin Tumbuns kusa da tafkin Chadi.
Daraktan yaɗa labarai na hukumar Air Vise Marshal Edwar Buba ne ya sanar da haka, a wata sanarwa day a fitar wanda y ace an kai harin ne a jiya Lahadi.

Rundunra ta gano ma ɓoyar tasu ne bayan bincike da samun bayanan sirri, sannan sun samu dammar tarwatsasu tare da lalata makamansu.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya na fama da hare-haren mayaƙan Boko Haram tsawon lokaci, wanda rundunar ke ci gaba da bayyana hallaka da dama tare da karɓar tubabbu daga cikinsu.