Wasu Manyan kwamandojin boko haram biyu sun mika wuya ga jami’an sojin hadin gwiwa na MNJTF da ke yankin Kasar Chadi.

Babban jami’in yada labaran rundunar Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.


Sanarwar ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun mika wuya ne ga rundunar sashi na Uku na rundunar a yau Talata.
Sanarwar ta ce kwamandojin da rundunar ta kama sun hada da Ibrahim Muhammad da Auwal Muhammad Wanka.
Abubakar ya ce samun nasarar na zuwa bayan jami’an sun matsa da kaiwa sansanonin ‘yan ta’addan hare-hare a cikin daji.
Sanarwar ta kara da cewa a tambayoyin da aka yiwa mutanen sun bayyana cewa sun shafe sama da shekara 15 su na aikata ta’addanci a cikin kungiyar Boko haram.
Daga karshe Kakakin ya bayyana cewa jami’an sun kwato bindiga kirar AK47 guda biyu, jigida guda Takwas, harsasai 191, Rediyo guda daya da dai sauransu