Babban hafsan sojin ƙasar Najeriya Taoreed Lagbaja ya ce sojojin da aka yi wa kisan gilla sun bar zawarawa matansu ɗauke da juna biyu sannan ga ƴaƴa.

Matan sojin guda 10, sannan sun bar ƴaƴa 21.


Janar Lagbaja ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen jana’izar sojin da aka yi wa kisan gilka a jihar Delta.
An hallaka sojin ne su 17 , a ranar 14 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki.
Sannan sun bar matansu da juna biyu, yayin da wata ke ɗauke da cikin watanni huɗu , da mai wata biyar sai mai watanni takwas.
Sai dai shugaban sojin ya ce rundunar ba za ta bar iyalan su tozarta ba.Sannan za su yi duk mai yuwuwa don ganin ab samar musu rayuwa mai inganci tare da barin kyakkayawan tarihi.
An dai yi jana’izar sojin ne yau Laraba a maƙabartar sojoji da ke Abuja wanda wasu shugabanni su ka halarta.