Shugaban Najeroya Bola Ahmed Tinubu ya halarci jana’izar sojoji 17 da aka hallaka a jihar Delta.

 

An yi jana’izar tasu ne a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja yau Laraba.

 

Shugaban ya halarci maƙabartar da misalin karfe 04:10pm na yamma.

 

Sannan ya samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya, ministan tsaro, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya.

 

Haka kuma akwai gwamnoni da su ka hakarci jana’izar ciki har da gwamnan Kano, Delta, Kogi, Imo, da gwamnan jihar Bayelsa.

 

An yi faretin girmamawa ga sojojin da aka yi ea kisan gilla a jihar Delta bayan da su ka je domin aikin wanzar da zaman lafiya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: