Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce wajibi ne a hukunta ƴan bindiga matsayin ƴan ta’adda muddin ana son samun nasara don daƙilesu.

Tinubu na wannan bayani ne yayin buɗe baki da ma’aikatan shari’a a Najeriya wanda ya gudana a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.


A sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya ce wajibi ne a hukunta masu garkuwa a matsayin ƴan ta’adda.
Dangane da batun albashin ma’aikatan shari’ar, shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yuwuwa don ganin ta inganta albashinsu da kula da walwalarsu.
Haka kuma zai tabbatar an samu cigaba cikin sauri a ɓangaren.
Sannan shugaban ya yabawa ma’aikatan shari’ar dangane da sadaukarwa da jajircewar da su ke yi don hidimtawa ƙasa.