Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da bukukuwan sallah karama cikin nutsuwa da kwanciyar hankali a fadin Jihar.

Gwamna Jihar Mai Mala Buni ne ya bayyana hakan a gurin wani taron majalisar tsaro da shugabannin hukumomin tsaro da suka gudanar a Jihar a ranar Litinin.

A yayin taron gwamnan ya ce an jibge jami’an tsaro a dukkan sassan Jihar, domin kula da muhimman guraren da mutane ke zuwa don gudanar da bikin sallah domin ganin an tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan ya ce jami’an tsaron za su kasance ne kafin ranar Sallar harma da bayanta.

Gwamnan ya kara da cewa jami’an hukumomin tsaro daban-daban ne aka girke a domin tabbatar da tsaro a Jihar, kuma yin hakan zai taimaka matuka wajen dakile duk wani yunkuri na batagari a Jihar a yayin gudnar da bukuwan sallar

Leave a Reply

%d bloggers like this: