Majalisar zartarwar Jihar Jigawa ta kafa wani kwamitin mai dauke da mutane shida da zai yi aikin gano yadda aka karkatar da kudade a shirin ciyar da mabukata a watan Azumin Ramadan a karamar hukumar Babura ta Jihar.

Kwamishinan yada labarai matasa da wasanni na Jihar Sagir Musa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Kwamishinan ya ce an bai’wa kwamitin wa’adin kwanaki bakwai da ya kammala bincike tare da mika rahoton binciken ga majalisar.

Kwamishinan ya bayyana cewa kwamitin ya kunshi shugaban ma’aikatan Jihar a matsayin shugaban kwamitin da kuma sauran mutane biyar a matsayin mambobi.

Kafa kwamitin da majalisar ta yi na zuwa ne bayan da gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya dakatar da kwamishinan kasuwanci na Jihar Alhaji Aminu Kanta, bisa zarginsa da ake da karkatar da kudaden da aka fitar domin ciyar da mabukata a watan Azumin Ramadan a karamar hukumar ta Babura.

Gwamna Namadi ya dakatar da kwamishinan ne nan take a ranar Jumu’a har zuwa lokacin da kwamitin zai kammala bincike akansa.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: