Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan ramadan da bukukuwan karamar sallah da aka gudanar a yau Laraba.

Mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a shafinsa na facebook.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya ja hankulan al’ummar musulmi da su kasance masu son juna, kyauta, sanin ya kamata, kishin kasa da kuma zaman lafiya da aka koya a cikin watan na Ramadan.

Sannan gwamnan ya bukaci al’ummar Jihar da su yiwa jihar da kasar addu’o’in samun zaman lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: