Gwamnatin Jihar Kano ta bai’wa mazauna gidan ajiya da gyaran hali na Jihar tallafin kayan abinci da shanu domin gudanar da shagulgulan bikin karamar sallah kamar kowa.

Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ne ya mika kayan ta hannun shugabar kwamitin nemawa daurarru afuwa ta Jihar Azumi Namadi Bebeji.

Azumi ta bayyana cewa gwamnatin ta yi hakan ne domin sanya farin ciki a zukatan daurarrun, domin suma mutane ne kamar kowa.

A yayin mika kayan shugaban kula da gidan gyaran halin na Kano Sulaiman Inuwa ya bayyana cewa kayan tallafin zai sanya daurarrun kasancewa jakadu nagari bayan sun shaki iskar ƴanci.

Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga gwamnan na Kano, tare da bayyana cewa sun shirya tsaf domin hada gwiwa da gwamnatin wajen ganin an yiwa kowa adalci a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: