Kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) ta mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmai murnan bukukuwan karamar sallah.

Shugaban kungiyar Daniel Okoh shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook a yau Laraba.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa bikin na karamar sallah na da matukar muhimmanci, wanda ba iya Musulmai kadai abin ya shafa ba harma da dukkan ‘yan kasar baki daya.

CAN ta kuma bukaci al’ummar Musulmai da su yi riko da dukkan abubuwan da suka koya a cikin watan ramadan domin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a fadin kasar.

Sannan kungiyar ta yi kira ga musulmai da su yi amfani da bukukuwan gurin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar, da kuma kawo karshen nuna bambance-bambance a tsakanin addinai guda biyu.

Daga karshe kungiyar ta bukaci shugabannin kasar da su inganta rayuwar ‘yan kasar wajen tabbatar da adalci a tsakaninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: