Rundunar sojin saman ta kasa ta yi nasarar hallaka wasu ‘yan ta’adda fiye da 11 a Jihohin Katsina da Borno.

Mai magana da yawun rundunar Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Edward ya ce jami’an rundunar sun kai hare-haren ne a kauyen ‘Yar Tsamiya a karamar hukumar Danmusa dake Jihar Katsina, inda jami’an suka hallaka sama da ‘yan bindiga 11.

Kakakin ya ce rundunar ta samu nasarar ne karkashin rundunar sojin saman ta Operation Hadarin Daji da Operation Hadin Kai a ranakun Jumu’a da Asabar.

Kazalika Edward ya ce jami’an sun kuma hallaka ‘yan ta’adda da dama a kauyen Grazah a karamar Hukumar Gwoza dake jihar Borno a wani ruwan wuta da aka yi musu.

Sannan ya ce jami’an rundunar sun kuma lalata makaman da ‘yan ta’adda ke amfani da su da guraren da suka mayar maboyarsu a Grazah.

Kakakin ya ce rundunar ta samu nasarar ne da taimakon bayanan sirri da ta samu.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: