Wasu da ba a san ko su waye ba sun hallaka wasu manoma biyu sannna su ka yi garkuwa da wani bayan sun jikkata wasu a jihar Benue.

 

 

 

Manoman dai ƴan gudun hijira ne da su ka bar gidajensu daga Umodigi a gundumar Entekpa ta ƙaranar hukumar Otukpo a jihar.

 

 

 

Rahotanni sun ce an kashe manoma biyu sannan aka yi garkuwa da guda ɗaya bayan an jikkata biyu.

 

 

 

Wani da ya ke bayani kan lamarin, ya ce manoman sun yi gudun hijira ne sanadin hare-haren da ake kaiwa, sai dai daga bisani sun yi shawarar zuwa gonakin nasu kuka su ka gamu da ajalin nasu a ranar Talata.

 

 

 

Wani da ya tattauna da ƴan jarida ta wayar tarho ya ce masu garkuwa sun buƙaci a basu kuɗin fansa naira miliyan biyar

 

 

 

Ya ce dukkanin waɗanda lamarin ya rutsa daa su ƴan gudun hijira ne.

 

 

 

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo ya tabbatar da faruwar lamarin yau Alhamis.

 

 

 

Ya ƙara da cewa yan bindigan sun kuma kai wani harin ƙauyen Upu domin yin ramuwar gayya a harin da sojoji su ka kai musu ranar Laraba.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: