Wasu jagororin jam’iyyar APC a Jihar Ondo sun zargi gwamnan Jihar Lucky Ayedatiwa akan kulla makarkashiya akan zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Afrilu da muke ciki.



Jagororin jam’iyyar karkashin wata kungiya mai rajin tabbatar da shugaban nagari a Jihar sun ce gwamnan na kokari sauya zaben na fidda gwani.
Shugaban kungiyar Evangelist Tade Ojo ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikewa da shugaban kasa Bola Tinubu kan lamarin.
Shugaban ya ce gwamnan tare da magoya bayansa sun buga katuna da tambarin jam’iyyar su na rabawa mutanen da ba mambobin jam’iyyar ba.
Shugaban ya bukaci jam’iyyar APC ta kasa da shugaban kasa Tinubu da su dakatar da Ayedatiwa akan yunkurin tarwatsa zaben na fidda gwani.
