Rahotanni da ke nuni a wannan lokaci an sake samun katsewar hasken lantarki a Najeriya bayan da rumbun samar da wutar na ƙasa ya sake lalacewa.

Matsalar ta auku ne da misalin ƙarfe 2:42 na dare wayewar yau Litinin.

Lalacewar ya haifar da ƙarancin wuta na faɗuwar megawatt 64.70.

Yyain da yake tabbatarwa da jaridar Daily Trust batun, shugaban DisCo a Jos Dakta Adakole Ejihah ya ce lamarin ya faru, kuma ana fatan shawo kan matsalar ba da jimawa ba.

Wannan shi ne karo na shida da babban rumbun samar da wutar ya samu matsala a shekarar 2024 da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: