Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wani dalibin jami’ar Ahmad Bello da ke garin Zariya mai suna Usman Adamu mai shekaru 34 bisa zargin batawa wani baturen ‘yan sanda mai suna CSP Danladi Muhammad suna a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Ahmad Muhammad Wakil ne ya bayyana hakan ta cikin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook.
Kakakin ya ce dalibin ana zarginsa da batawa jami’in suna ne a shafinsa na facebook, inda ya wallafa rubutun yin barazana da tsoratarwa ga jami’in.

Jami’in ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike akan dalibin har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci.

Wasu Rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa a Jihar sun farwa Baturen na ‘yan sandan saboda bayanan da Usman Adamu ya wallafa a kansa, inda wasu jami’an ‘yan sanda suka kubutar da shi.