Babban hafsan sojojin Kasa Najeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi alkawarin cewa rundunar sojojin Najeriya ba za ta gaza ba wajen kawo karshen ‘ƴan ta’addan da suka addabi kasar ba.

Lagbaja ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wajen rufe taron hafsan sojojin Kasar na shekarar 2024 a birnin tarayya Abuja.

Taoreed ya bayyana cewa rundunar su ba za ta gaza ba wajen zakulo duk wani batagari a Kasar tare da kawo karshensu a fadin Kasar.

Hafsan ya kuma yi kira ga masu aikata laifuka da kuma sauran masu son kawo cikas ga zaman lafiyar Kasar da su shiga cikin hankalinsu ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Sannan hafson ya yi kira ga ‘yan kasar da su ci gaba da goyawa rundunar tasu baya a kokarin da ta ke yi na samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi al’mma.

Hafsan ya kuma bukaci jami’an da su kara jajircewa akan ayyukan su domin ganin sun ga bayan ‘yan ta’adda a Kasar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: