Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu ciki har da wani dalibin jami’a a lokacin da ‘yan bindiga suka kai musu hari a ranar Alhamis a jihar Filato.

Maharan sun hallaka mutanen ne a lokacin da suka kai musu hari a kauyen Butura da ke cikin karamar hukumar Bokkos ta Jihar da misalin karfe 9:00, inda zuwan su ke da wuya suka bude wuta akan mutanen kauyen.
Rahotanni sun bayyana cewa dalibin da harin ya rutsa dashi ya na aji na biyu ne a jami’a, inda ya ke karantar fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa.

Wasu majiyoyi daga kauyen sun bayyana cewa bayan hallaka dalibin hakan ya sanya daliban jami’ar suka gudanar da zanga-zangar.

Jihar Filato dai na daya daga cikin Jihohin Najriya da ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan ta’addan a yankunan Jihohin Kasar.