
Hukumar kashe gobara a Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku yayin da su ke ƙoƙarin ɗakko wayar salula daga cikin shadda.
Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau Lahadi

Ya ce tun da farko sun samu kiran waya daga wajen wani Aminu Yar Gwanda wanda ya basu labarin cewar wani dattijo mai shekaru 60 Malam Danjuma wanda aka fi sani da Black cewar ya faɗa cikin shadda yayin da wayarsa ta faɗa.

Bayan da ya kasa fitowa yayansa uku su ka bishi domin fito da shi, amma biyu da mahaifin su ka rasu yayin da aka ceto guda.
Al’amarin da ya faru a ƙaramar hukumar Taanyawa a Kano, Jami’an sun miƙasu wajen yan sanda yayin da aka garzaya da su asibitin Bichi.