Shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe korafe na Kano, Muhyi Rimingado ya bayyana yadda suka zakulo wasu makudan kudi.

Muhyi ya ce hukumar ta gano N51.3bn wanda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya karkatar.
Shugaban hukumar ya bayyana haka ne yayin hira da ‘yan jaridu inda ya ce kudin na daga cikin N100bn da aka ware na kananan hukumomi.

Ya ce an tura kudin ne zuwa kananan hukumomi kafin a hada baki da wasu ma’aikata inda aka karkatar da kudin.

Rimingado ya ce kusan mutane 200 sun tabbatar da yadda gwamnatin Ganduje ta tilasta su yin karya kan yadda aka kashe kudin a lokacin.
Ya kara da cewa Ganduje ya siyar da wani kamfani mallakin gwamnatin jihar kan farashin kudi abin takaici ga iyalansa.
Ya bayyana cewa sun tanadi gamsassun hujjoji da za su yi amfani da su domin shigar da kara.