Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya bukaci gwamnonin jihohi da su tallafi harkokin lantarki a ƙasar domin samun wadatacciyar wutar lantarki a ƙasar.



Shettima y ace ya zama wajibi gwamnoni su shiga cikin lamarin tare da bayar da gudunmawarsu, domin a yanzu ƙasa da kashi 20 na yan kasar ne ke morar wutar lantarkin a kasar.
Haka zalika kashi 45 na ƴan kasar ba sa samun damar alaƙa ko morar wutar lantarkin baki ɗaya.
Shettima na wannan bayani ne yayin taron karawa juna sani da kuma jin ra’ayi wanda wakilai a zauren majalisar ƙasar su ka shirya.
Ya ce a wannan lokaci akwai buƙatar a duba halin da wutar ke ciki domin samar da mafita.
Mataimakin shugaban kasar wanda mai bashi shawara kan harkokin lantarki Sadik Wanka ya wakilta.
Bayanin dai ya ci kawo da batun ministan makamashi a Najeriya ya bayar a byaa cewar kaso sama da 80 na ƴan ƙasar na morar hasken lantarki.