Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya roki yan Najeriya da su kara hakuri a kan wahalar rayuwa da ake ciki.

 

Mataimakin shugaban kasar ya ce dukkan tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta fito da su musamman janye tallafin man fetur, an kawo su ne domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar.

 

Kashim ya ce lalle nan kusa kadan da zarar an magance matsalolin da ake fama dasu ‘yan Najeriya za su sha dara.

 

Ya kara da cewa nan kusa za a ga canji nagari cikin rayuwar al’ummar kasar ta hanyar rage talauci, wadatar abinci da haɓakar tattalin arziki.

 

Mataimakin shugaban kasan ya yi jawabin ne a jiya Alhamis, 2 ga watan Mayu a wani taro da aka shirya a dakin taro na Ladi Kwali da ke Abuja.

 

 

 

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana aniyarsa ta yin hadaka da kasar Hungary a fannin tsaro da noma.

 

A cewar ministan, yunkurin da suka yi yana daga cikin bada muhimmanci da gwamnatin Bola Tinubu ta yi wurin samar da cikakken tsaro a Abuja.

 

Mista Wike ya bayyana kudurin ne yayin wata ziyara da ya kai ofishin jakadancin kasar Hungary dake Abuja.

 

A lokacin ziyarar, ministan ya bayyana abubuwan da gwamnatin ke buƙata daga kasar Hungary domin dakile barazanar tsaro a Abuja.

 

Ya lissafa bukatar samun jirage marasa matuka da za su rika samar da cikakken tsaro a birnin tarayyar.

 

Amma sai dai ya ce akwai bukatar a tantance irin jiragen da za su dace da birnin domin kaucewa ɓacin rana da kuma kasancewarsu ingantattu.

 

Mista Wike ya kara da cewa lalle akwai matsalar tsaro a Abuja amma da yardar Allah za su magance ta idan suka samu hadakar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: