Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe wani kwamandan na rundunar hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC a jihar Benue.

 

Kwamandan da ƴan bindigan suka hallaka an bayyana sunansa a matsayin Mike Ode.

 

Jaridar Punch ta ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Shaapera da ke ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar.

 

Kawun marigayin, Nicholas Ode, ya bayyana cewa an kashe ɗan uwansa ne a ƙauyen Shaapera da ke ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a ranar Litinin.

 

Ya ƙara da cewa an ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Benue da ke Makurdi.

 

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar NSCDC, Mike Ejelikwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutuwar jami’in ba za ta hana rundunar gudanar da aikinta na samar da tsaro ga duk wani ɗan kasa mai bin doka da oda a jihar ba.

 

Ya ƙara da cewa marigayin ya rasu yayin artabu da ƴan bindiga sannan ya tabbatar da cewa an yi wa ƴan bindigan illa sosai.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: