Kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sauye-sauyen haraji ya ce akwai bukatar a kara yawan kudin da ake karba na harajin wato VAT.

Kwamitin ya ba da shawarar sake waiwayar harajin kashi 7.5% na yanzu da ake karba daga abokan ciniki tare da neman a kara kudin domin daidaita tattalin arziki.


Da yake jawabi a taron fayyace manufofi da tasirin binciken kwamitin, shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa za a sake duba tsarin raba kudaden shiga na VAT.
Manema labarai sun ruwaito Oyedele ya ce kwamitin ya bayar da shawarar kara kason kudin VAT da ake ba kananan hukumomi da jihohi zuwa kashi 90% daga kashi 85% na yanzu.
Bisa ga sashe na 40 na dokar harajin VAT, gwamnatin tarayya na samun kashi 15% na kudaden harajin, jihohi suna karbar kashi 50%, sannan kananan hukumomi suna karbar kashi 35%.
Sannan ya bayyana cewa sabon tsarin rabon kudin harajin VAT yana ba da fifiko ga kananan hukumomi domin haraji ne da ake tattarawa a matakin jihohi.
Gwamnatin taohon shugaba Muhammadu Buhari ce ta kara kudin harajin VAT daga kashi 5% zuwa kashi 7.5% yayin da hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) take karba idan aka siyo kayayyaki da kuma sayar da su.