Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya zargi gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da hannu wajen ta da yamusti yayin zanga-zangar yunwa jihar.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Kano ta ce an sace tadardun zargin da ake yi masa da matarsa da dansa wanda aka shigar da kara a gaban kotu.


Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da hannu wajen tada hargitsi don bata gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ganduje ya yi zargin yau a Abuja a wata sanarwa da saataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC ta ƙasa Edwin Olofu ta sanyawa hannu.
Ya ce sun samu bayanai na ƙarƙashin ƙasa wanda au ka gano gwamnn jihar Abba Kabir Yusuf ne ya ɗauki nauyin zanga-zangar don bata gwamnatin tarayya.
Ya ce gwamnan ya dauki nauyin rikicin wanda ya yi silar rasa rayuka da asarar dukiya.
Ya ce sun yi Alla Wadai da lamarin wanda aka yi yunkurin ruguza Kano.
Dangane da batun da gwamnatin Kano ta yi na sace takardun tuhuma da ake yiwa tsohon gwamnan Kano a babbar kotun jihar, Ganduje ya ce abin dariya ne.