Jam’iyyar NNPP ajihar Kano ta ayyana naira 600,000 amatsayin kuɗin sayen fom ɗin takarar shugaban ƙaramar hukumar yayin da masu neman kujerar kansila za su sayi fom kan kuɗi naira 200,000.
Shugaban hukumar a jihar Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a jihar yau Talata.
Ya ce jamiyyar na yin duk mai yuwuwa wajen ganin sun shiga zaɓen na dukkani gurbin da ake da su.
Sai dai ya buƙaci ƴan takarar da su ke riƙe da muƙamai zaɓaɓɓu ko waɗanda aka naɗa da su ajiye muƙamansu don cika sharuɗan hukumar zaɓe ta jihar Kano.
Ya ce hakan zai tosheduk wata ƙofa da za ta haifar da tazgaɗo tare da biyayya ga ƙa’ida da dokokin hukumar zaɓen
Dangane da batun naira miliyan goma matsayin kuɗin fom ɗin takara ga masu son tsayawa shugabancin ƙaramar hukuma da kuma naira miliyan biyan ga masu son tsayawa takarar kansila, shugaban jam’iyyar ya ce hukumar zaɓen ta ayyana ne domin tabbatar da cewar masu kishi da son tsayawa takarar kuma su ka cancanta ne a kai.
Shugaban ya ce jam’iyar NNPP ta mayar da hankali ne wajen harkar ilimi da talafawa matasa don su dogara da kansu.
Haka kuma jam’iyyar za ta tantance ƴan takarar a ɓangaren ilimi.


