Hukaumar kula da Yanayi ta Kasa NIMET ta gargadi wasu daga cikin Jihohin Kasar Shida kan barazanar fuskantar tsawa da iska mai karfi a lokacin da mamakon ruwan sama zai zuba a Jihohin a kwanaki masu zuwa.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafawa a shafinta na X a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa za a fuskanci a hakan ne a Jihohin Arewacin Kasar.

Ta ce daga cikin Jihohin da abin ya shafa sun hada Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Zamfara, da kuma Sokoto.

NIMET ta kara cewa a hasashen da ta gudanar ruwan saman da za a gudanar a Jihohin ka iya haifar da Ambaliya.

Hukumar ta kuma bukaci al’umomin Jihohin da sa kula matuka, tare da yin shiri domin fuskantar barazanar.

NIMET ta yi kira ga mazauna yankunan da suka saba ganin ambaliyar ruwa da su kyaucewa guraren, tare da bin umarnin hukumomin da abin ya shafa domin tsera daga matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: