Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya lashi takobin kama fitaccen mai garkuwa da mutanen nan Bello Turji.

Janar Chiristopher Musa ya umarci jami’an soji da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kama Bello Turji.
Babban hafsan tsaron ne ya bayyanawa manema labarai haka yau a Abuja, ya ce ba da jimawa ba za su tabbatar sun kamashi.

Dangane da dokokin da Bello Turji ya sakawa mutanen wasu ƙauyuka, Janar Chiristopher Musa ya ce su na aiki da sauran jami’an tsaro kuma za su tabbatar an basu kariya.

Ya yi kira ga mutanen ƙauyukan da su basu haɗin kai, a cewarsa, haɗin kan da mutanen zasu bayar shi ne zai taimaka wajen samun nasara.
Kuma ya sake tabbatar da cewar za su kama Bello Turji cikin kankanin lokaci.
Sannan su na aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro don ganin an samar da zaman lafiya a Najeriya.