Fadar shugaban Najeriya ta ce za a yi sauye sauye a mukaman da shugaban ya bai wa masu dafa masa sha’anin mulkin ƙasar.

Da alama dai za a tantance kokarin murraban gwamnatin bisa kwazon kowa daga bayanan da su ke bai wa shugaban ƙasar a kowanne wata.
Batun ya fito ne daga hadiman shugaban ƙasa Bayo Onanuga da O’Tega Ogra yayin taron manema labarai a Abuja.

Onanuga ya ce shugaban ƙasar ya shida cewar zai yi duba ga mukarrabansa, kuma tabbas zai yi.

Sai dai y ce ba shi da masaniya ko zai yi hakan ne kafin watan Oktoba.
A nasa bangaren, Ogra ya ce za a tantance kwazon mukarraban gwamnatin ne bisa kwazon aikin kowa daga rahotannin da su ke kaiwa.
Shugaba Tinubu dai na shan suka daga jamiyyun hamayya har a da jamiyyarsa tare da kira a gareshi don sauke dukkanin ministocinsa da ba sa tabuka komai.
kwazon yan majalisar zararwar shugaban ƙasa