Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce an samu raguwar shigo da man fetur Najeriya da lita biliyan 3.5 a shekara guda.

Wani rahoto da hukumar ta fitar jiya Talata, ta gani cewar a shekarar 2023 an shigo da mai lita biliyn 20.30 yayin da a shekarar 2022 aka shigo da lita biliyan 23.54 wanda ke nuni da cewar an samu raguwar shigo da shi da kaso 13.77 tsakanin shekarun.
An dai samu ƙarancin shigo da man fetur tun bayn da gwamnatin tarayya ta fara yunƙurin cire tallafin man fetur.

Yayin da aka kara samun karancin shigo da shi bayn da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da cewar ba zai ci gaba da biyan tallafin man fetur ba.

A halin yanzu kuwa man fetur na a kasuwa domin yi wa kansa da kansa farashi.