Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana jami’an hukumar kula da lafiyar ababen hawa ta VIO kamawa, tsarewsa ko cin tarar ababen hawa.

Kotun karkashin mai sharia Juctice Evelyn Maha, ya yanke hukuncin ne a jiya Laraba
Ya ce a tsarin doka hukumar ba ta da hurumin kwacewa, kamawa ko cin tarar direbobi baya tsaresu a kan tituna.

Alkalin ya gamsu da korafin da wani Attorny Marshal ya shigar a gaban kotun.

Wanda ya ce yin hakan take hakkin dan adam ne.
A hukuncin da kotun ta yanke a jiya, ta hana jami’an na VIO kamawa, tsarewa ko cin tarar dorebobi.
Kotun ta ce hakan ya sabawa dokar aikinsu kuma karya doka ne.
A don haka ne ma kotun ta haramtawa jami’an.