Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bai wa dilallan man fetur izinin fara siyo mai kai tsaye daga matatar mai ta Dangote.

 

Gwamnatin ta ce daga yanzu ba sai dilallan mai sun tuntubi kamfanin mai na ƙasa NNPC ba.

 

A wata sanarwar da ministan kudi Wale Edun ya fitar yau, ya ce majalisar zartarwa ta kasa ta amince dilallan man su fara siyo man kai tsaye daga matatar ba tare da tuntubar NNPC ba.

 

A baya dilallan man na aika da bukatar siyo man ta shafin NNPC, bayan da NNPC ya fara siyo man daga matatar mai ta Dangote.

 

Dilallan sun koka kan tsaron da su ke samu kafin samun man fetur ɗin.

 

Sai dai a halin yanzu gwamnatin ta sahale musu fara siyo man kai tsaye daga matatar Dangote.

Leave a Reply

%d bloggers like this: