Masana sun yi hasashen cewar farashin kan fetur na iya sake hauhawa a Najeriya.

Dakta Muda Yusuf masanin tattalin arziki ya rikicin da ke faruwaa a gabas ta tsakiya da yakin da ke faruwa tsakanin Iran da Israela na iya sake sakawa farashin man fetur ya sake hauhawa.


Haka kuma yadda darajar naira ke sake faduwa a kasuwar hada hadar kudi hakan na iya sake jefa naira cikin wani hali wanda ka iya shafar man fetur.
Sannan farashin gangar mai na dada hauhawa wanda shi ma hanya ce da dalilin iya karuwar farashin a Najeriya.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne aka wayi gari da sabon farashin man fetur wanda kamfanin mai na Nnpc ke siyar da lita guda naira 1,030 a Abuja yayin da ake siyaarwa naira 1,070 a Kano.
Batun da mutane ke kokawa a kansa har ma aka yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta mayar da tsohon farashin.
Karin da aka sake samu dai ya haifar da cece kuce ga yan kasar har ma da manyan yan siyasar Najeriya.