Rundunar yan sanda a jihar Ogun ta kaddamar da farautar mutanen da ake zargi da hallaka dan takarar kansila na jam’iyyar APC a jihar.

An hallaka Adeleke Adeyinka a jiya Asabar.

Adeleke na neman kujerar kansila a gunduma ta 15 da ke karamar hukumar Abeokuta ta kudu.

Rahotanni sun ce an harbe Adeyinka ne sannan ana dinga jifan kansa da dutse har sai da ya rasa ransa.

Mai magana da yawun yan sanda a jihar Ogun Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar hakan.

Sannan ta ce ana zargin yan kungiyar asiri da kisan mutumin mai shekaru 40.

Tuni aka mika gawarsa ga iyalansa.

Sannan sun kaddamar da bincike tare da farautar wadanda ake zargi da aikata kisa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: