Mataimakin shugaban kasar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya ce shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai dakile matsalar rashin aikin yi da kaso mai yawa.

Shettima ya bayyana haka ne a wajen wani taro da aka yi a jihar Nassarawa jiya Asabar
Ya ce salon mulkinsu zai wadata yan kasar da aikin yi daban daban daga gida da kasashen ketare.

Dangane da batun matasa da ba sa samun aikin yi bayan kammala karatu har ma da wadanda ba su yi karatu ba, ya zama wajibi a rage karuwarsu wajen samar da ayyukan yi.

A cewarsa, ya na daga cikin manufofi na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu samar da aikin yi don bunkasa tattalin arzikin kasa.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Nassarawa ya godewa dukkanin masu ruwa da tsaki da ke tallafawa sabon tsarin HCDP don inganta tattalin arziki.
Sannan ya ce za a saka matasa a harkokin noma, lafiya da sauran ayyukan dogaro da kai domin dorewar tsarin.