Kwamishinan shari’a a jihar Delta Mista Ekemejero Ohwovoriolehe ya bukaci jami’an tsaro da su fara yin bincike kafin sakawa wanda ake zargi ankwa a hannu.

Kwamishinan ya yi kiran ne a taron karawa juna sani n yini guda da aka yi a Asaba.
Ya ce wajibi ne a dakile kura kurai da ake yi musamman wajen binciken manyan laifuka domin ciyar da bangaren shari’a gaba.

A cewarsa dalilin taron shi ne samar da hanyoyin bincike masu sauri ta hanyar amfani da sabbin dokokin shari’a.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro musamman yan sanda su ne mabudi a harkar tafiyar da shari’a.
Sannan ya ce zai sake bude kofofin ganawa da shi ga dukkanin jami’an tsaro da lauyoyi.
Sannan ya ja hankalin jami’an tsaron da su guji saurin sakawa wanda ake zargi ankwa a hannu har dai idan ya yi kokarin guduwa.
