Hukumar haana fasa kwauri a Najeriya kwastam ta ce za ta yi amfani da fasahar zamani wajen hana fasa kwauri a iyakokin kasar

Hukumar shiryyar kudu maso yamma ce ta sha alwashin wanda ta ce za a samu ingantaccen tsaro tare da dakile hanyoyin fasa kwauri a iyakokin yankin.

Mataimakin ahugaban hukumar da ke kula da shiyyar kudu maso yamma Saidu Abba Yusuf ne ya bayyana haka a Abeokuta ta jihar Ogun yayin da ya ziyarci ofishinsu a jihar

A cewarsa, a halin yanzu su na iya kokarinsu wajen ganin sun inganta tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani don sake bayar da tsaro a iyakokin don hana fasa kwauri.

Sannan ya sha alwashin bai wa jami’an horo a kai a kai don tabbatar da nasarar aikin.

Sannan ya hori jami’an da su kasance masu aikin da kearewa a duk inda suke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: