Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta sanya ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2025 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben gwamnan Jihar Anambra.

Shugaban hukumar ta INEC na Kasa Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, a yayin wani taro na musamman da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasar kasar masu rajista, wanda ya ce zai kasance na karshe a shekarar 2024.

Farfesa Yakub ya ce za a fitar da sanarwar zaben a hukamance a ranar 13 ga Nuwamba mai kamawa ta shekarar 2024.

Shugaban ya kara da cewa hukumar ta INEC tana sanya ran jam’iyyu za su gudanar da zabukan fidda gwani daga ranar 20 ga watan Maris din 2025 zuwa ranar 10 ga watan Afrilun shekarar.

shugaban ya ce za a bude shafin da za a sanya bayanan ɗan takara da misalin ƙarfe 9.00 na safe a ranar 18 ga watan Afrilu 2025 kuma za a rufe da misalin ƙarfe 6.00 na yamma a ranar 12 ga Mayu 2025.

Sannan ya kara da cewa hukumar za ta fitar da sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 9 ga watan Yunin 2025, yayin da za a fara yakin neman zabe daga ranar 11 ga Yuni, har zuwa ranar 6 ga Nuwamba 2025.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: