Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya TCN ya ce tsaffin kayan aikin da ake dasu ne ya sa wutar kasar ke yawan lalacewa

 

Sannan ya ce zai samar da wata hanya da za ta kawar da shiga duhu bayan wutar kasar ta samu matsala.

 

Shugaban kamfanin Sule Abdulaziz ne ya tabbatar da haka yayin ganawa da shi a gidan talabiji na Channels.

 

Ya yi zargin cewar lalacewar wutar da ake yawan samu a kasar na da nasaba da tsaffin kayan aiki da ke amfani dasu fiye da shekara 50.

 

A cewar shugaban, su na kan tattaunawa da bankin duniya domin yin wani aiki da zai shafe shekara biyu wanda a yanzu aka ci nasarar kammala kaso 70 a cikinsa

 

Ya ce aikin zai taimaka wajen hana ƴan ƙasar shiga cikin duhu yayin da aka samu katsewar lantarki daga manyan tashoshin samar da wuta.

 

Ya ce su na kokarin sabunta hanyoyin kai wutar lantarki ko a cewar gwamnatin ba ta da isassun kudaden da za su kammala aiki.

 

Amma su na haɗa kai da kamfanoni masu zaman kansu don samun kuɗaɗen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: