Gwamnatin tarayya ta dakatar da dukkan zarge-zargen da take yiwa jami’in kamfanin Binance Tigran Gambaryan.

Gwamnatin ta dakatar da tuhume-tuhume ne da take yiwa jami’in na Binance ne a safiyar yau Laraba, bayan da lauyan hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ya shigar da kara gaban kotu, inda kuma daga bisani ya shaidawa kotun cewa hukumar ta dakatar da zargin da take yiwa jami’in na Binance.

A yayin dakatar da karar lauyan ya bayyana cewa Gambaryan wanda ya kasance dan kasar Amurka ne kuma ma’aikacin kamfanin Binance ne ana tuhumar shi ne da ayyukan da suka shafi kamfanin kan badakalar kudi.

Lauyan wanda ake kara ya amince da kudurin lauyan na EFCC, inda ya ce Gambaryan ba shi da hannu a manyan hukunce-hukuncen kudi na Binance.

Gwamnati ta dakatar da tuhume tuhumen ne bayan watannin da suka gabata ana tattaunawa domin sasanta tsakanin Najeriya da Amurka don ganin an saki dan kasar.

Idan ba a manta ba watanni bakwai kenan jami’in na Binance Gambaryan ke tsare a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja kan tuhume tuhumen da suka shafi safarar kudi.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: