Shugaba Bola Tinubu ya rushe wasu daga cikin Ma’aikatun da ministocinsa Ke jagoranta.

Mai magana da yawun shugaban na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hakan a yau Laraba.

Bayo ya ce shugaban da Majalisar zartarwa ta Kasa sun amince da rushe wasu daga cikin ma’aikatun Kasar ne a yayin da shugaban ya jagoranci zaman majalisar zartarwar ta Kasa da aka gudanar a Abuja yau.

Sanarwar ta Bayo ta kara da cewa majalisar ta amince da rushe ma’aikatar wasanni tare da mayar da ayyukanta karkashin Hukumar Kula da Harkokin Wasanni.

Yayin da majalisar ta sake amincewa da rushe Ma’aikatar Bunkasa Ci-gaban Arewa da takwarorinta na sauran yankuna.

Sanarar ta ci gaba da cewa shugaban ya rushe Ma’aikatar bunkasa ci gaban Neja Delta da Ma’aikatar Bunƙasa ci gaban Kudu maso yamma.

Inda ya ce shugaban ya bayyana cewa za a kafa sabuwar hukumar bunƙasa ci gaban Yankuna da za ta jagoranci ayyukan ma’aikatun yankunan Arewa ta Gabas da arewa maso Yamma.

Kazalika Tinubu ya kuma hade ma’aikatar yawon bude idanu da ta al’adu da samar da tattalin arziki ta Kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: