Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da wasu Ministocinsa biyar daga bakin aiki.

Tinubu ya sallami Ministocin ne a yau Laraba, a yayin taron majalisar zartarwa ta Kasa a Abuja.
Ministocin da shugaban ya sallama daga bakin aiki sun hada da Minista Ilmi Tahir Mamman, Ministar harkokin mata Uju-Ken Ohanenye, Ministan yawon buɗe ido Lola Ade-John, Karamin Ministan gidaje da raya birane Abdullahi T Gwarzo da kuma Ministar matasar Jamila Ibrahim.

Sai dai bayan sallamar Ministocin Biyar daga bakin aiki shugaban ya maye gurbinsu da wasu.

Kazalika bayan rusa ma’aikatar harkokin wasanni shugaba Tinubu ya nada Shehu Dikko a matsayin shugaban hukumar wasanni ta Kasa.
Shugaban ya kuma amince da nadin Bianca Odinaka Odumegu-Ojukuwu a matsayin Karamar Ministar harkokin waje, sai Dr Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan jin kai da walwala , yayin da Muhammadu Maigari Dingyadi zai rike ma’aikatar ayyuka ta kwadago.
Sauran su ne Dr Jumoke Oduwole zai rike ma’aikatar kasuwanci da zuba hannun jari, yayin da Idi Mukhtar Maiha shima zai rike ma’aikatar cigaban kiwon dabbobi, Yusuf Abdullahi Ata zai rike mukamin karamin Ministan gidaje da raya birane, ya yin da Suwaiba Sa’id Ahmad za ta rike mukamin karamar Ministar ilimi.
Sannan shugaban ya kuma mika godiyarsa ga ministocin da ya dakatar daga bakin aiki bisa hidmar da suka yiwa gwamnatinsa dama kasar baki daya, tare da yi musu fatan alkhairi a cikin rayuwarsu, tare da bayyana cewa Kasar ba za ta manta da gudummawar da suka bata ba.
