Tsohon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga a Najeriya Muhammad Nani ya ce mutane ba su fahimci sabon tsarin haraji da ake son yi wa gyaran fuska a majalisa ba

A cewarsa, sabon tsarin zai amfanar da kowanne ɓangare na Najeriya.
Muhammad Nani ya ce kuskuren fahimta ne yadda wasu ke tunanin tsarin zai amfanar da jihohin Legas da Rivers kaɗai maimakon ƙasa baki ɗaya.

Ya ce tsarin zai taimaka wajen amfanar da kowanne ɓangare tare da samun wani kaso ga ɓangaren da su ke da ƙarancin kuɗaɗen shiga

Ya ƙara da cewa ya karanta sabuwar dokar da ake son yi wa gyara, ya misalta hakan da damar cin gashin kai da aka bai wa ƙananan hukumomi a Najeriya wanda ya ce shi ma tsari ne dai zai amfanar da ƙasar baki ɗaya
Muhammad Nani ya ce bayan suka da tsarin ya fara damu wasu daga cikin ƴan majalisar tattalin arziki sun fara janyewa daga goyon bayan tsarin, sai dai sun buƙaci a sake shigar da masu ruwa da tsaki don ci gaba da fahimtar dokar.
Idan za a iya tunawa, kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya sun yi watsi da tsarin har ma gwamnan jihar Borno ya ce idan aka tabbatar da shi ba za su iya biyan ko da albashi ba.
Kudirin dai ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar dattawa.
A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barai I. Jibrin, ya ce an yi wa dokar karatu na biyu ne don bayar da dama ga masana don yin bincike tare da nazartar sabuwar dokar.
“Ba za a iya bayar da damar yin nazarin dokar ba har sai an yi mata karatu na biyu, a don haka ba gaggawa mu ka yi ba, batu a kan hakan ma yanzu aka fara ba wai an gama ba” in ji Barau.
A cewar tsohon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa Muhammad Nani, sashe na 77 da ake magana a kai na cikin dokar na iya ɗaukar shekaru uku zuwa kafin kafin fara aiwatarwa.
Sannan ya ce batun bayar da kuɗaɗen shiga ga jihohin da ke da rigistar kamfanoni ita ma an sauya ta, yadda jihar da aka shigar da kaya za ta samu kaso mai yawa
A cewarsa, sabuwar dokar za ta ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga jihohi tare da tallafawa wadanda su ke samun karancin kudaden shiga daga asusun rarraba arzikin ƙasa.